News
Kotu Ta Yanke Wa Manajan Bankin FCMB Ɗaurin Shekaru 121 A Gidan Yari
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mai shari’a S. N. Odili na babbar kotun jihar Anambra da ke zaune a garin Onitsha ya yankewa tsohon manajan bankin First City Monument Bank, FCMB reshen Onitsha, Nwachukwu Placidus, ɗaurin shekara 121 a gidan yari bisa samunsa da laifin karkatar da kuɗaɗen wasu Kwastomomi kimanin N112,100,000 .
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa an gurfanar da shi ne tun a ranar Talata, 27 ga watan Maris, 2018, a kan tuhume-tuhume 16 da suka haɗa da damfara,da kuma sata.
Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Shirinta Na Sake Duba Farashin Lasisin Hakar Ma’adanai
Mai laifin dai ya amsa laifin sa ne ta hanyar matsin lamba da ya sha a hannun hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon ƙasa EFCC shiyyar Enugu.
Daga cikin tuhume-tuhumen da ake masa“Nwachukwu Placidus tsakanin watan Fabrairu 2009 zuwa Nuwamba 2014 a Onitsha, jihar Anambra da ke karkashin ikon babbar kotun jihar Anambra ta Najeriya ya yi yinƙurin sace kuɗi (N112,100,000) miliyan dari da goma sha biyu. Da kuma Naira Dubu Dari daga bankin Idemili Microfinance Bank bisa karyar cewa ya sanya wadannan kuɗi a wani asusu na ajiya da First City Monument Bank PLC, wanda hakan ke nuna cewar ya sani ya take doka.
