News
Ya kamata a kawo ƙarshen wahalhalun da ƴan Nigeria ke ciki _kakakin majalisun jahohi 36 ga tinubu
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Kakakin majalisun jihohi 36 sun bukaci shugaba Bola Tinubu da ya samar da tsare-tsare masu dorewa da za su kawo ƙarshen wahalhalun da ƴan Najeriya ke ciki.
Anyi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta kuma kakakin majalisar dokokin jihar Oyo, Hon. Adebo Ogundoyin, a karshen taron da masu jawabi 29 suka halarta a babban burnin tarayya Abuja.
Ta kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin Jihohi da su samar da tsare-tsare masu dorewa tare da jajircewa wajen magance radadin da al’umma ke ciki. Musamman a wannan lokaci
Jaridar daily post ta rawaito cewa Kwamitin yace Hakan ya samo asali ne daidai lokacin da aka shiga mashasshara tattalin arziki da Kum cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi da kuma kawo wa kasuwannin canji, cikas lamarin da ya jawo wa al’umma fadawa mummunar yanayi
sanarwar,a gurin taro ta Kuma ce ta amince da jajircewar shugaban kasa kan manufofinsa na inganta tattalin arziki da aka dauka kawo yanzu, kamar cire tallafin man fetur da kuma tafka caccakar farashin canji, sakamakon da ba a yi niyya ba na wadannan manufofin ya yi tsanani matuka.
Da yake jawabi a wajen taron, Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Tajudeen Abbas, wanda ya samu wakilcin shugaban kwamitin majalisar mai kula da huldar ‘yan majalisar Hon Mark Esset, ya bayyana cewa, za a ba da fifiko kan batun ‘yancin cin gashin kan ‘yan majalisun dokoki na jihohi a aikin sake duba kundin tsarin mulkin kasar da ake yi, inda ya kara da cewa zai kasance cikin muhimman batutuwan da suka shafi majalisar.
A Taron an tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi Yadda za,a Samar da shugabanci na gari a ƙasar
