Connect with us

News

Ƙananan Hukumomin Kano 14 Na Fuskantar Iftila’in Ambaliyar Ruwan —Hukumar  NiMET

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa (NiMET), ta gargadi wasu kananan hukumomi 14 daga cikin 44 na Jihar Kano, cewar za su iya fuskantar iftila’in ambaliyar ruwa a damina mai zuwa.

Advertisement

Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin ko’odinetan shiyyar Kano da Jigawa, Dokta Nuradeen Abdullahi, a yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan ambaliyar ruwa.

Ya kamata a kawo ƙarshen wahalhalun da ƴan Nigeria ke ciki _kakakin majalisun jahohi 36 ga tinubu

Kananan hukumomin da za su iya fuskantar barazanar sun hada da Rimin Gado, Tofa, Kabo, Madobi, Garum Malam, Bebeji, Rano, Dawakin Kudu, Warawa, Wudil, Sumaila, Ajingi, Kura da Dala.

Advertisement

Sauran kananan hukumomin guda biyar su ne, Karaye, Takai, Bunkure, Dawakin Tofa, da Makoda, sai dai su ana hasashen ambaliyar ba lallai ta girmama kamar ta sauran ba.

Babban abin jan hankali a nan shi hanyoyin da za a bi domin magance barazanar aukuwar ambaliyar ruwa a daminar da ke tafe.

Advertisement

Leadership ta ruwaito cewa Dakta Abdullahi ya jaddada muhimmancin hada hannu da hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Kano (SEMA), domin tabbatar da cewa masu ruwa da tsaki sun shirya tsaf domin dakile barazanar.

“Mata da yara kanana sun fi zama masu rauni a lokacin damina,” in ji Dokta Abdullahi.

Advertisement

Amma ya bukaci mazauna yankunan da ka iya fuskantar ambaliyar ruwan, da su zauna cikin shiri da kuma bin matakan kariya.

Da ta ke bayani dangane da lamarin, kwamishiniyar jin-kai da kawar da talauci ta jihar, Hajiya Amina Abdullahi, ta tabbatar da kokarin gwamnatin jihar na hana aukuwar ambaliyar ruwan.

Advertisement

Ta ce gwamnatin ta kafa wani kwamiti mai karfi, karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, wanda aka dora wa alhakin tsaftace magudanan ruwa a dukkanin kananan hukumomin jihar domin dakile hatsarin ambaliyar ruwa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending