News
Kungiyar kiristoci CAN ta kaddamar da sabbin shuwagabannin, gudanarwar ta a Jahar Adamawa
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN reshen jihar Adamawa ta kaddamar da zababbun shugabanninta.
Sabbin shugabannin da za su yi aiki na tsawon shekaru biyar, sun hada da Rev. Joel Danjuma Manzo, Shugaban; Rev Victor Saje, mataimakin shugaba; Rev. Emeka Obionyo, Sakatare; Rev. Gambo Bupwada, Mataimakin Sakatare; da Rev. Malacy Wache, Treasurer.
Haka kuma an kaddamar da bikin wanda ya gudana a cocin St Monica Lutheran Church of Christ in Nigeria, LCCN, da ke Jimeta, dake Jigar Yola Adamawa
Jaridar daily post ta rawaito Shugabancin ya kunshi kananan hukumomin kungiyar inda – Barista Victor Eze a matsayin Darakta a harkokin shari’a da jama’a; da Fasto Ishaku Shehu, Darakta a al’amuran da suka shafi Jiha da walwala.
Sauran sun hada da Evangelist Haruna Donge a matsayin Daraktan Tsare-tsare, Bincike da Dabaru, yayin da David Simon Dzalla zai kasance Daraktan Ilimi, Mata da Matasa.
Da yake jagorantar bikin kaddamarwar, shugaban CAN na kasa, Archbishop Daniel Okoh, wanda ya samu wakilcin sakataren kungiyar na kasa, Farfesa Samson Fatokun, ya ce hedkwatar CAN ta kasa tana da yakinin cewa sabbin mambobin za su yi aiki tukuru domin ganin kungiyar ta cigaba da samun cigaba sannan Kuma ta Ya bukace su da su yi adalci wajen gudanar da ayyukansu.
Shima Mataimakin gwamnan jihar Adamawa, Farfesa Kaletapwa Farauta, wanda ya samu wakilcin kwamishinan mata na jihar, Wunfe Anthony, ya yi kira ga malaman addini da su ci gaba da inganta zaman lafiya tare da bayar da goyon bayan da ya dace domin sabbin mambobin kungiyar ta CAN don samun nasara.
Sabon shugaban kungiyar CAN na jihar, Rev Joel Manzo, ya yi kira ga daukacin al’ummar jihar da su zauna lafiya da juna.
Sannan Ya yi alkawarin tabbatar da gadon tsohon shugaban CAN na jihar, Bishop Stephen Mamza wanda ya kasance Bishop na Katolika na Yola
