News
Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Hana Belin Wani Babban Jami’in Crypto Gambaryan
DAGA YADIR SANI ABDULLAHI
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Juma’a, ta ki amincewa da neman belin wani babban jami’in kamfanin crypto, Tigran Gambaryan.
Mai shari’a Emeka Nwite, yayin da yake yanke hukuncin ya ce an ki amincewa da bukatar belin ne saboda ya bi sahun bukatar da aka gabatar a gabansa a tsanake tare da yanke shawarar cewa wanda ake tuhuma zai tsallake beli idan har aka amince da shi.
Kungiyar kiristoci CAN ta kaddamar da sabbin shuwagabannin, gudanarwar ta a Jahar Adamawa
Channelstv ta ruwaito cewa Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta gurfanar da Gambaryan, kamfaninsa, Binance Holdings Limited da kuma wani babban jami’in gudanarwa a halin yanzu, Nadeem Anjarwalla, da laifin karkatar da kudade da kuma bada tallafin ta’addanci.