News
Jam’iyyar APC Ta Shirya Tsaf Za Ta Fara Neman Wanda Zai Maye Gurbin Ganduje
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Da Dukkan alamu dai fadar shugaban ƙasa ta baiwa masu ruwa da tsaƙi damar fara neman wanda zai maye gurbin shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje
Duk da irin shiru da Fadar shugaban ƙasa ta yi kan kan cece-kucen da aka yi ta yi akan Ganduje ,kwatsam sai rahotanni suka bayyana cewar an baiwa gwamnonin jam’iyyar APC na shiyyar Arewa ta Tsakiya damar fara neman sabon shugaban daga yankin kamar yadda jam’iyyar ta tsara tun farko.
Gwamnatin Tarraya Za Ta Buɗe Shafin Neman Bashin Ɗalibai Cikin Mako Mai Zuwa
Wata majiya mai tushe ta shaida wa Jaridar LEADERSHIP a yau Juma’a cewar baya ga baiwa shiyyar Arewa ta tsakiya damar fara neman sabon shugaba, akwai yuwuwar fadar Shugaban ƙasa za ta baiwa Congress for Progressive Change (CPC) damar zaƙulo wanda zai maye Ganduje.