Politics
Jam’iyyar APC Ta Shirya Shiga Zaben Shugabannin Kananan Hukumomi da Kansiloli A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano Karkashin Jagorancin Abdullahi Abbas, ta bukaci al’ummar Kano da mambobin jam’iyyar da suke sha’awar tsayawa takarar shugabancin ƙaramar hukuma da Kansila da su miƙa takardar sha’awarsu ga ofisoshin jam’iyyar dake Kananan Hukumominsu.
Jam’iyyar na sanar da cewar tun daga ranar 12 zuwa 14 ga watan Satumba Ofisoshin jam’iyyar APC su kasance a buɗe domin karɓar masu sha’awar tsayawa takara, tun daga karfe 8 na safe zuwa 5 na yamma.
Sanarwa na dauke dasa hannun Hon. Ahmad S. Aruwa, Kakakin Jam’iyyar APC na Kano.