Connect with us

News

Nuna Alhini Da Jajantawa Al’ummar Jihar Borno A Bisa Jarabawa Da Allah Ya Saukar — Imam Murtadha Gusau

Published

on

FB IMG 1725980656574

 

DAGA IMAM MURTADHA GUSAU

Advertisement

 

Da Sunan Allah Mai Rahama, Mai Jinkai

Advertisement

 

Assalamu alaikum

Advertisement

 

Ya ku bayin Allah! Kididdigar hukuma ta nuna cewa, mutum dari biyu da ashirin da tara (229) ne suka mutu, mutane dubu dari uku da tamanin da shida da dari biyu da talatin da tara (386,239) suka zama ‘yan gudun hijira (IDPS), sannan gidaje dubu casa’in da hudu da dari hudu da casa’in da biyu (94,492) ne suka lalace sanadiyyar ambaliyar ruwan sama, a tsakankanin jihohi ashirin da tara (29), na fadin Najeriya, kuma a cikin watanni tara.

Advertisement

Wannan ya kasance ne a kididdigar da hukumar bayar da agajin gaugawa ta gwamnatin tarayya, wato NEMA ta fitar. Kuma wannan kididdiga ta nuna cewa, arewa maso gabas (North East) da arewa maso yamma (North West) sune suka fi ko wane bangare na kasar nan shiga wahala sanadiyyar wannan ibtila’i na ambaliyar ruwa.

Yan Najeriya 400 Da Aka Ta Tiso Ƙeyar Su Daga Hadaddiyar Daular Larabawa Sun Isu Filin Jirgin Saman  Abuja

Muna addu’a da rokon Allah ya sawwake muna wannan jarabawa, amin.

Advertisement

‘Yan uwa masu girma, ana cikin wannan ne kuma, kwatsam, sai Allah Subhanahu wa Ta’ala cikin ikon sa, ya jarabi al’ummar jihar Borno da wani irin mummunan ibtila’in ambaliyar ruwa, sanadiyyar fashewar Dam din Alau.

Wanda kashi saba’in cikin dari na Birnin Maiduguri wannan ambaliya ta shafe shi.

Advertisement

Sama da gidaje dubu dari biyu sun samu matsala. Abubuwan more rayuwa duk sun rushe. Post office, Maiduguri teaching hospital duk sun shiga cikin wannan ibtila’in.

Muhimman wurare da suka hada da wani sashe na fadar Shehun Borno, Babbar Kasuwar Maiduguri da asibitin kwararru na jami’ar Maiduguri duk sun samu matsala.

Advertisement

Wuraren da wannan ibtila’i ya shafa sun hada da, anguwar GRA da gidan Zoo na Maiduguri da College of Nursing da College of Agriculture da School of Health Technology.

Wuraren da wannan jarabawa ta fada wa sun hada da, State Secretariat da Makabarta da Lagos area da anguwannin Bulabulin, Gwange da kofar Shehu.

Advertisement

Allah yayi muna maganin wannan ibtila’i, amin.

Ya ku bayin Allah! Wallahi duk irin yadda zamu bayyana maku adadi da yawan asarar da aka yi a wannan jarabawa ta ambaliyar ruwa a jihar Borno, Allah ya sani ba zamu iya ba, domin gaskiyar lamari shine, kawai dai abun sai wanda ya gani.

Advertisement

Kawai muna dai matukar nuna damuwar mu da alhini, tare da jajantawa al’ummar garin na Maiduguri bisa wannan jarabawa da Allah Subhanahu wa Ta’ala ya jarabe su da shi.

Daukacin jama’ar wannan Babban Masallaci namu mai albarka, da wannan cibiya ta yada addinin Musulunci da ke nan garin Okene, ta jihar Kogi, muna jajantawa gwamnatin jihar Borno da masarautar jihar Borno da dukkanin al’ummar jihar Borno da kewaye, bisa wannan jarabawa ta ambaliyar ruwa da ya afka masu sanadiyyar fashewar wannan Dam na Alau.

Advertisement

Muna matukar nuna tausayi da alhini da jajantawa tare da addu’ar Allah ya kiyaye na gaba, amin.

Wadanda suka rasu Allah ya gafarta masu. Dukkanin waɗanda suka yi asarar dukiyoyi kuma, muna addu’a da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala ya mayar masu da mafificin alkhairi duniya da lahira.

Advertisement

Kuma lallai ya kamata kuma ya dace gwamnatocin tarayya da na jihohi, da masu hannu da shuni da ‘yan kasuwa da kamfanona da kungiyoyi, su haɗa hannu, su hada ƙarfi da ƙarfe wajen tallafawa wadannan bayin Allah da wannan lamari ya shafa, domin Allah!

Annabi Muhammad (SAW) yace:

Advertisement

“Duk wanda ya taimaki wani mutum dake cikin damuwa, ya yaye masa damuwa, shi ma Allah zai yaye masa damuwar duniya da ta lahira. Duk wanda ya yaye wa wani mutum wani bakin ciki, shi ma Allah zai yaye masa bakin cikin duniya da lahira. Allah yana taimakon bawan sa, matukar bawa yana taimakon bayin Allah.”

Don haka, mu taimaka wa dukkanin wasu bayin Allah da muka san suna bukatar taimako, a duk inda muka same su, domin Allah.

Advertisement

Mu sani, abunda ka taimaki wani da shi, shine naka, wanda kuma kaci ba naka bane.

Allah ya taimake mu, amin.

Advertisement

 

Wassalamu alaikum,

Advertisement

 

Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi Najeriya. Za’a iya samunsa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending