News
Gwamnatin Tarraya Za Ta Buɗe Shafin Neman Bashin Ɗalibai Cikin Mako Mai Zuwa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Asusun Kula da Bashin Karatu ga Dalibai na Najeriya (NELFUND), ya ce zai buɗe shafin neman bashin karatu ga ɗaliban ƙasar da ke sha’awar karɓar bashin a ranar 24 ga watan Mayu domin su cike.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun asusun, Nasir Ayitogo ya fitar ya ce bayan buɗe shafin ɗalibai za su iya neman bashi domin ci gaba da biyan kuɗin karatunsu ba tare da wata matsala da ta danganci kuɗi ba.
Hukumar dake kula da gidajen gyaran hali ta dakile yunkurin shigar da miyagun ƙwayoyi gidajen yari
“Shafin zai kasance mai sauƙin ta’ammali, ta yadda ɗaliban za su iya cike shi cikin sauki tare da aikewa da buƙatarsu ba tare da wata tangarɗa ba”, in ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma yi kira ga duka ɗaliban ƙasar da suka cancanci cin bashin karatun da su yi amfani da wannan dama wajen gyara makomarsu da kuma ci gaban ƙasar baki ɗaya.
”Daliban za su iya samun shafin a kan wannan adireshi: http://nelf.gov.ng domin fara cike buƙatarsu da zarar lokacin ya yi”, in ji sanarwar.
A shekarar da ta gabata nedai shugaban ƙasar Bola Tinubu ya ɓullo da tsarin bayar da bashi ga ɗaliban ƙasar domin samun damar faɗaɗa karatunsu a manyan makarantun ƙasar, a wani mataki na rage wa ɗaliban wahalhalun da suke fuskanta da suka danganci kuɗi.
