Sports
Kurunkus: Mbappe Ya Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Komawa Real Madrid Da Taka Leda

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Kylian Mbappe ya saka hannu kan ƙwantiragin komawarsa Real Madrid daga Paris St-Germain,
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa yarjejeniyarsa ta kare ranar 30 ga watan Yuni da Tsohuwar Kungiyar ta Paris St-Germain .
Tun cikin watan Fabrairu ɗan ƙwallon tawagar Faransa ya amince baka da baka da cewar zai koma Sifaniya, sannan cikin watan Mayu aka sanar da zai bar PSG a karshen kakar wasa ta bana.
Hukumar Hisbah Ta Cika Hannu Da Jarumin TikTok Al’ameen Wanda Aka Fi Sani Da G-fresh A Kano.
Mbappe mai shekara 25 ya saka hannun kan ƙunshin yarjejeniyar da Real Madrid ta gabatar masa, wanda zai koma Sifaniya ranar 1 ga watan Yuli da za a buɗe kasuwar cinikayyar ƴan ƙwallo a La Liga.
Ana sa ran Real Madrid za ta sanar da labarin kammala ƙulla ƙwantiragi da Mbappe a mako mai zuwa daga nan ta gabatar da shi gaban magoya baya a Bernabeu kafin fara Euro 2024.
Mbappe ya lashe kofin duniya a 2018, kuma shi ne kan gaba a yawan cin ƙwallaye a PSG mai 256 a raga, tun bayan da ya koma ƙungiyar aro daga Monaco a 2017.
Ya amince da yarjejeniyar da za ta kare a Real zuwa karshen 2029, zai ke karbar £12.8m a kowacce kaka da karin ladan £128m da za a biya cikin shekara biyar, kuma zai rike kudin tallace-tallacensa.
Ɗan kasar Faransa zai samu damar buga tamaula tare da Luca Modric, yayin da ɗan ƙwallon Croatia zai kara sa hannu kan yarjejeniyar kaka ɗaya a Real Madrid.
Real Madrid ce ta lashe La Liga na bana na 36 jimilla da tazarar maki 10 tsakani da Barcelona, wadda ta yi ta ukun teburin babbar gasar tamaula ta 2023/24.