Sports
Real Madrid ta lashe Gasar Zakarun Turai (Champions League), karo na 15 a tarihinta.

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta lashe Gasar Zakarun Turai (Champions League), karo na 15 a tarihinta.
Madrid ta doke Dortmund a wasan karshe na gasar wanda aka yi a filin wasa na Wembley da ke Birtaniya.
Dalilai 14 da Gwamnatin Tarraya ta bayar kan dagewarta akan mafi karancin albashi na N60,000
Ƙwallon da ɗan wasan bayan Real Madrid, Dani Carvajal ya zura a minti na 74 da kuma wadda Vinicius Junior ya zura a minti na 82 ne, suka bai wa ƙungiyar damar sake kafa wani sabon tarihi a gasar.
Dortmund dai ba ta taɓa lashe gasar ba, inda a baya ta sha kashi a hannun Bayern Munich da ci ɗaya mai ban haushi a shekarar
Gasar Zakarun Turai dai ta zama gasar da Real Madrid ta gagara a ciki, inda ta ke ci gaba da yin warkajaminta.