Connect with us

Sports

A Yau Za’a Buga Wasan Karshe Na Kofin Zakarun Nahiyar Turai

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Za’a fafata wasan ne tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real madrid ta kasar andulus da kungiyar kwallon kafa ta Borusia Dortmond ta kasar Jamus.

Advertisement

Wasan zai wakana a babban filin wasa na kasa da kasa na kasar Ingila wato Wembley, karkashin jagorancin alkallin wasa slavko vincic dan asalin kasar Slovenia da misalin karfe 8 na dare.

Gwamnatin  Shugaba Tinubu za ta sake duba yadda gwamnatin Buhari ta jinginar da filayen jiragen sama biyu

Wannn shi ne karon farko Real Madrid da Borussia Dortmund za su kara a wasan karshe a babbar gasar tamaula ta Turai, amma karo na 15 da za su fuskanci juna a gasar.

Advertisement

Real madrid ce kan gaba da jumullar kofina 14 yayinda Dortmond take da guda 1 amma tana fatan lashe na 2 a tarihi. musamman la’akari da tayi wajen doke madrid da ci 4 da nema ta hannun tsohon dan wasanta Robert Lewendoski.

Ƙungiyar da Edin Terzic ke jan ragama ta kai wannan matakin, bayan da ta kai zagaye na biyu daga rukuni na shida, sannan ta fitar da PSV a zagayen ƴan 16.

Advertisement

Haka kuma Dortmund ce ta yi waje da Atletico Madrid a zagayen quarter-finals, sannan ta yi nasara a daf da karshe a kan Paris St Germain gida da waje.

Ƙungiyar Dortmond ta kai zagaye na biyu daga rukuni na shida, sannan ta fitar da PSV a zagayen ƴan 16, kuma ta yi waje da Atletico Madrid a zagayen daf dana karshe sannan ta yi nasara a wasan kusa dana karshe a kan Paris St Germain gida da waje.

Advertisement

Itama kungiyar ta Real madrid tayi nasara akan manyan kungiyoyi wadanda suka hada da kungiyar manchester city a wasan kusa dana karshe sannan ta doke Bayern munich a wasan daf dana karshe.

Shin menene ra’ayinku dangane da wannan babban wasa?

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending