News
Gwamnatin Shugaba Tinubu za ta sake duba yadda gwamnatin Buhari ta jinginar da filayen jiragen sama biyu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bayyana cewa Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za a sake bibiyar kwangilar jinginar da Filayen jiragen sama guda biyu, wanda gwamnatin Buhari ta yi.
Keyamo ya bayyana haka a Abuja, a taron Majalisar Zartaswa ta Ƙasa.
Majalisar Dattawa Ta Fara Yunkurin Ragewa Karfin Fada Ajin Da CBN Ke Da Shi
“Za mu sake ko sabunta kwangilar jinginar da filayen jiragen biyu, domin a fito da komai a yi komai keƙe-da-ƙeƙe.
Ya ce har yanzu haka an dakatar da batun kafa Nigerian Air.
Ya ƙara da cewa Jirgin Kamfanin Ethiopian Airlines ne tsohon Ministan Hadi Sirika ya shafa wa fenti da tutar Najeriya, ya ƙaddamar da shi.
“Tilas Nigerian Air ya zama na cikin gida kacokan”, inji Keyamo.
Cikin shekarar da ta gabata ne tsohon Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika ya yi gidogar ƙaddamar da Nigerian Air, Kwanaki biyu kafin ya sauka daga minista.
Premium Times ta ruwaito cewa Kwanan nan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin sa da na ‘yar sa, bayan an damƙe shi ana neman Naira biliyan kusan 20 a hannun sa.
-
News6 days ago
Gwamnatin Kano Ta Umarci Masu Talla Da Masu Sana’ar Jari Bola Su Bar Karkashin Gadar Tal’udu
-
News3 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
