Connect with us

News

A Karshe Dai Abba Kyari Ya Shaki Iskar Ƴanci Bayan Shafe Watanni 27 A Gidan Yari

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

An sako tsohon kwamandan rundunar ‘yan sandan fikira Abba Kyari daga gidan yarin Kuje da ke Abuja.

Advertisement

Hakan ya biyo bayan hukuncin da wata babbar kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke na bayar da belin Kyari na tsawon makonni biyu.

A Yau Za’a Buga Wasan Karshe Na Kofin Zakarun Nahiyar Turai

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa da yake bayar da belin a ranar 22 ga Mayun 2024, Mai shari’a Emeka Nwite ya ce makonni biyun za su ba Kyari damar yin jana’izar mahaifiyarsa da ta rasu a ranar 5 ga watan Mayu.

Advertisement

Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar ya shafe watanni 27 a gidan yari.

Sai dai kakakin rundunar babban birnin Tarayya NCoS Adamu Duza ya ce an saki Kyari ne bayan ya cika sharuddan belin sa.

Advertisement

Da yake magana a ranar Juma’a Duza ya ce “DCP Kyari ya cika sharuddan belinsa kuma tun yau aka sake shi.”

Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta kama Kyari a ranar 14 ga Fabrairun 2022 bisa zarginsa da hannu da wata kungiyar kwaya ta kasa da kasa.

Advertisement

An gurfanar da Kyari tare da jami’an ‘yan sanda hudu, Sunday Ubia Bawa James Simon Agirigba da John Nuhu a gaban kotu a ranar 7 ga Maris 2022.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending