Connect with us

News

Ya Kamata ’Yan Jarida Su Guji Rahotannin Da Ka Iya Haifar Da Tashin Hankali — KOMC ‎

Published

on

IMG 20260920 WA0036

Ƙungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo ta Kano Online Chapel (KOMC), ƙarƙashin ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), ta buƙaci ’yan jarida da su riƙa kiyaye ƙa’idojin aikin jarida, gaskiya, daidaito da adalci a yayin gudanar da ayyukansu.

‎Ƙungiyar ta yi wannan kiran ne a yayin babban taronta da aka gudanar ranar Asabar, 19 ga Satumba, 2026, a Sakatariyar NUJ da ke Kano.

Tsohon IGP Abba Ya Nemi Kafa Cibiyar Horar Da ’Yan Jarida A Radio Kano

‎A cikin wata sanarwa da ta fitar bayan taron, KOMC ta jaddada muhimmancin bin ƙa’idoji da ɗa’ar aikin jarida, tare da tabbatar da sahihancin bayanan da ake wallafawa.

‎Ta kuma buƙaci ’yan jarida su kasance masu adalci da daidaito, musamman wajen ruwaito harkokin siyasa da zaɓe, tare da guje wa rahotannin da ka iya haifar da tashin hankali ko zubar da mutuncin aikin jarida.

‎Sanarwar ta ce ya kamata ’yan jarida su sanya maslahar jama’a a gaba, tare da tabbatar da gaskiyar bayanan da suke yaɗawa a kafafen yaɗa labarai, musamman kafafen intanet.

Advertisement

‎KOMC ta ce bin ƙa’idojin aikin jarida da ɗabi’un sana’ar zai taimaka wajen kare martabar aikin jarida da kuma ƙara amincewar jama’a da kafafen yaɗa labarai.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending