Connect with us

News

KANO:Wata Mata Ta Hallaka Mijinta Saboda Zai Mata Kishiya A Rogo

Published

on

An kama wata mata mai suna Bilkisu Sani a ƙaramar hukumar Rogo ta Jihar Kano, bisa zargin kashe mijinta, Hafizu Gausu, wanda rahotanni suka ce yana shirin ƙara aure.

Lamarin ya faru ne a yankin Katsalle da ke garin Rogo da misalin ƙarfe 7:00 na daren Juma’a.

Tsohon IGP Abba Ya Nemi Kafa Cibiyar Horar Da ’Yan Jarida A Radio Kano

Wani mazaunin yankin, Auwal Kazagi Rogo, ya shaida wa Daily Trust cewa mazauna yankin sun garzaya wurin bayan sun ji kukan matar marigayin, wadda ta yi ihu tana cewa an yanka mijinta.

Sai dai, bayan da suka isa wurin, sun tarar da Gausu da mummunan rauni a kansa, inda daga bisani ya rasu. Rahoton ya kuma ce an ga wata alamar cizo a kunnensa.

Bayan faruwar lamarin, mazauna yankin sun sanar da ’yan sanda, inda jami’an suka isa wurin tare da ɗaukar gawar marigayin domin gudanar da bincike kan musabbabin mutuwarsa.

Advertisement

’Yan sanda sun kama Bilkisu a matsayin babbar wadda ake zargi da hannu a lamarin, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano ainihin abin da ya faru.

Rahotanni sun ce marigayin yana shirin ƙara aure, lamarin da ake zargin ya haifar da rashin jituwa tsakaninsa da matar tasa kafin faruwar lamarin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending