News
Ba Gaskiya Ba Ne Cewa Ni Ne Mamallakin Wajen Haƙar Ma’adinan Matasan Neja 37 —IBB
Tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya), ya musanta zargin cewa shi ne mamallakin wurin haƙar ma’adinan da wasu matasa 37 suka rasa rayukansu a Jihar Neja.
An kama matasan ne bisa zargin gudanar da aikin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, kafin daga bisani aka samu rahoton mutuwarsu a hannun jami’an Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Nijeriya (NSCDC).
Ya Kamata ’Yan Jarida Su Guji Rahotannin Da Ka Iya Haifar Da Tashin Hankali — KOMC
Wakilin IBB, Dakta Ɗanladi Umar Abdulhameed, ya bayyana zargin da cewa ba shi da tushe, yana mai cewa tsohon shugaban mulkin sojan ba shi da wata alaƙa da wurin haƙar ma’adinan ko kuma lamarin da ya shafi mutuwar matasan.
Martanin na zuwa ne bayan wani mutum da ya tsira daga lamarin, Malam Babawo Tudun Nasera, ya yi iƙirarin cewa wurin haƙar ma’adinan mallakin IBB ne.
Nasera ya yi wannan ikirari ne yayin da yake bayar da labarin yadda jami’an tsaro suka kama masu haƙar ma’adinan, ciki har da ɗansa, Salim, wanda daga baya ya rasu.
A cewar Nasera, an taɓa dakatar da su daga aiki a wurin, amma daga bisani aka ba su damar ci gaba da haƙar ma’adinan, inda ya yi ishara da cewa mai wurin na da alaƙa da IBB.
Sai dai Abdulhameed ya ce IBB ba shi da hannu a harkar wurin haƙar ma’adinan, yana mai kiran zargin da “ƙarya mara tushe.”
Ya kuma buƙaci a gyara rahotannin da suka danganta IBB da wurin, tare da kira ga jama’a da su yi watsi da zargin.
