Connect with us

News

Ƴan Sanda Sun Kama Ɗan Majalisa Kan Alaƙa Da Ƴan Bindiga A Zamfara

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Kwamishinan ƴan sandan jihar Zamfara, Muhammad Dalijan, ya sanar da kama wani ɗan majalisar dokokin jihar da kuma wani tsohon shugaban ƙaramar hukuma, bisa zargin su da alaƙa da ƴan bindiga masu garkuwa da mutane.

Advertisement

Dalijan ya bayyana haka ne ranar Laraba lokacin da ya karɓi bakuncin jami’in kula da sashin yaƙi da ta’addanci a karkashin ofishin Majalisar Dinkin Duniya kan yaƙi da miyagun ƙwayoyi da manyan laifuka Thomas Parker, a hedikwatar rundunar da ke Gusau, babban birnin jihar.

Mahaifi Ya Sayar Da ‘Ya’yansa Guda 5 Naira Miliyan Daya Da Dubu Dari 2, A Jihar Sakkwato

Sai dai kwamishinan bai bayyana sunayen dan majalisar da tsohon shugaban karamar hukumar ba, ko lokacin da aka kama su.

Advertisement

Dalijan ya kuma yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta taimaka wajen samar da dakin gwaje-gwaje na bincike domin kaucewa kalubalen zuwa Legas domin gudanar da binciken kwakwaf sannan kuma ya bukaci Majalisar da samar da, tsare-tsaren ta a Jihar  Zamfara irin wadda ta yi a Maiduguri ta jihar Borno.

 

Advertisement

Fri

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending