News
Yunwa Tayi Yawa: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jihar Legas A Safiyar Ranar Demokradiyya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Masu zanga-zangar, a safiyar ranar Laraba, sun yi dirar mikiya a karkashin gadar Ikeja da ke Legas, a daidai lokacin da Najy ke bikin ranar dimokuradiyya ta 2024.
Sai dai akwai jami’an tsaro sosai, yayin da aka hango ‘yan sanda da jami’an hukumar kiyaye zaman lafiya a unguwanne a Legas a wurin.
Zan Aike Wa Majalisa Ƙudiri Game Da Sabon Mafi Ƙarancin Albashin Ma’aikata — Shugaba Tinubu
Masu zanga-zangar, da yawansu, sun yi ta rera wakokin hadin kai yayin da suke rike da alluna da tutoci.
Wasu daga cikin kwalayen na da rubuce-rubuce kamar: ‘Shugaba Tinubu, karka bari talaka ya numfasa’, ‘Ga wani Biyan albashin ma’aikatan Najeriya yanzu.
Jaridar PUNCH Online ta rawaito cewa wasu kungiyoyin farar hula da suka hada da Take It Back Movement, the Education Rights Campaign, the Coalition for Revolution and the Socialist Workers League, ne ke jagorantar zanga-zangar.
