News
Shirin TMP Zai Taimaka Wajen Bunkasa Tattalin Arzikin Nijeriya
DAGA ABDULSALAM MAHMUD
A yayin da ake fuskantar kalubalen raguwar kudaden shiga bisa matsin tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta, gwamnatin tarayya ta samar da tsari dake cike da kyakkyawan shekaru 2 da suka gabata; wato tsarin zamanantar da kasuwanci na hukumar hana fasa kwauri wato Kwastam
An samar da tsarin ne domin kawo sauyi ga batun tattara haraji, da kuma rage dogaro da fannin mai wajen samar da kudaden shiga a Najeriya.
Yunwa Tayi Yawa: Zanga-zanga Ta Ɓarke A Jihar Legas A Safiyar Ranar Demokradiyya
Babban abinda shirin zai sa gaba shi ne bunkasa ayyukan hukumar hana fasa kwauri ta kasa wato Kwastam, mayar ra hankali wajen bunkasa samun kudaden shiga, kula da kasuwanci da yaki da cin hanci da rashawa a kasa.
Shirin wanda aka aiwatar da shi bisa tarin hadaka tsakanin gwamnati da bangarori masu zaman kansu na PPP an sanya hannu kan tsarin jinginarwa a ranar 30 ga watan Mayu na 2022 tsakanin gwamnatin tarayya ta hanyar hukumar gudanarwa ta hukumar kwastom da kamfanin dake kula da shirin na TMP.
Shirin ya fadada zuwa shigar da fasahar zamani cikin ayyukan hukumar kwastom wanda zai bada dama wajen gudanar da aikinta yadda yakamata.
A karkashin yarjejeniyar, kamfanin dake kula da shirin na TMP zai samar da dukkan abinda ke bukata ciki har da kula da na’urori da bada horo da kuma samar da tsarin fasahar sadarwa na zamani a tsawon shekarun da aka diba na jingina wato shekaru 20.
Amfanuwar da za a samu daga shirin:
1. Habbaka kudaden shiga ga gwamnarin tarayya ta hanya mai tsari fa dakile zurarewar kudade.
2. Shigar da tsarin zamanantarwa na hukumar kwastom domin lura da al’amuran kasuwanci
3. Aiwatar da matakan dakile fasa kwauri da kuma karfafa alaka da hukumomi da jami’an tsaro
4. Samar da tsari na bai daya kamar na UCMS da kuma na’urar bibiya ta zamani ga jiragen dakon kaya.
5. Kara tabbatar da bin dokoki da kuma rage sa baki don kawar da cin hanci da kuma kawo tsaiko
6. Bada horo ga jami’an hukumar hana fasa kwauri ta kasa ta hanyar shirye shirye na hadin gwiwaa.
Alfanun shirin ga Najeriya.
Shirin yayi alkawarin habbaka kudaden shiga ga gwamnatin tarayya inda ake sa ran samun harajin Dala biliyan 250 a tsawon shekarun da aka jingine.
Bugu da kari, zai sa Najeriya sahun gaba wajen amfani da fasahar zamani a batun kasuwanci na kasa da kasa da kuma habbaka kasuwanci tsakanin kasashe.
Shin tayaya shirin zai taimaki gwamnatin tarayya a fannin matsayarta kan haraji.
Shigar da kwastom tsarin fasahar zamani zai taimaka wajen bunkasa tattara kudaden shiga da kuma rage zurarewa kudaden shigar.
Shin hanyar jinginarwa ce mafi dacewa wajen cimma hakan?
Duba da bukatar zuba hannun jari na daban, bin matakin jinginarwa zai baiwa gwamnati damar rarraba hanyoyin samun kudin shigarta, da kuma bayar da kudade wadanda kai tsaye zasu bunkasa tattalin arziki.
Shin shirin zai hafar da rashin aiki ga wasu?
Ana saran shirin zai samar da sabbin aikin yi mussaman a batun taka rawa na masu amfani da shi. Irin shirin ya haifar da ci gaba a fadin duniya.
Bayanan rufewa.
Shirin zamanantar da kasuwanci na hukumar kwastom yazo a lokacin da ake bukatarsa wanda zai kawo sauyi ga tattalin arzikin Najeriya. Dole gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen ganin an aiwatar da shirin cikin nasara.
Mahmud, mataimakin Edita na PRNiger
ia ne ya rubuta cikin harshen Turanci.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
