News
EDIL-KABIR: Gwamnatin Kano Ta Ba Da Hutu A Makarantun Firamare Dana Sakandire A Fadin Jahar.
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Gwamnatin jihar Kano ta umarci dukkan makarantun firamare da na gaba da firamare da ke jihar da su ba da hutun Edil-Kabir daga ranar Juma’a 14 ga watan Yuni, 2024 zuwa Litinin 24 ga watan Yuni, 2024.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi Balarabe Abdullahi Kiru ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta kara da cewa, a saboda hakane ana bukatar iyaye da masu kula da daliban da ke makarantun kwana da su dauki ‘ya’yayenssu a safiyar Juma’a 14 ga watan Yuni, 2024.
Ya kuma yi Kara da cewa duk sauran tsare-tsaren Dake cikin jadawalin kalandar karatun makaranta ta 2023/2024 wadanda suka hada da ranar hutu na nan yadda yake a tsare.
Sanarwar ta ruwaito cewa Kwamishinan Ilimi, Alhaji Umar Haruna Doguwa ta bakin Daraktan wayar da kan jama’a yana kira ga iyaye da masu kula da su da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun dawo makaranta ranar da aka sanya dan cigaba da karatu.
Kasancewar za’a dauki matakin ladabtarwa a kan duk daliba ko dalibin da ya kasa komawa bisa ga sharuddan da aka gindaya a kwanan wata.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
