News
An Samu Gawar Ɗalibar Jami’ar ATBU A Banɗaki
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wata ɗalibar Kimiyyar Kwamfuta yar aji 300 a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi, Naja’atu Salisu ta rasu bayan an same ta a sume a wani banɗakin dalibai da safiyar Juma’a.
Rahotanni na nuni da cewa , Naja’atu ta shiga banɗaki ne na ɗakin kwanan dalibai mata da ke harabar jami’ar na Gubi domin yin wanka tare da shiryawa domin tafiya aji kamar yadda ta saba amma sai a ka ji ta shiru bata fito ba.
Wata abokiyar Naja’atu tace “ Ta gama duk shirye-shiryen tafiya aji da safe kafin ta shiga banɗakin. Hatta kayan da zaka saka ta fito dasu ta ajiye bakin gado da niyyar in ta fito wanka ta sanya su”
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin ATBU, Zailani Bappa, ya ce da faruwar lamarin an garzaya da ita asibitin jami’ar domin kula da lafiyarta, amma jami’an lafiya sun kasa gano wata jijiya a jikinta.
“Da su ka lura da haka, sai a ka garzaya da Naja’atu zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa inda likitoci su ka tabbatar da mutuwarta,” in ji shi.
Bappa ya ce an binne Naja’atu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
