Connect with us

News

Rundunar Ƴan Sanda Ta Kama Wani Dan Fashi Tare Da Ƙwato Miliyan 5 A Kano

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta ce ta cafke wani ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a karamar hukumar Kunchi, inda a tare da shi aka kwato sama da Naira miliyan 4 da bindiga kirar AK-47 guda biyu da harsashi guda 47.

Advertisement

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, a wata sanarwa da ya fitar a yau Talata, shi ne ya bayyana cewa an kama Hassan Iliya dan asalin jihar Katsina ne bayan sun kai wani hari a kauyen Yandadi inda suka yi fashin naira miliyan goma sha biyar.

Zanga Zanga: An shiga ganawar sirri tsakanin Sanata Ali Ndume da shugaban jam, iyyar APC

A cewarsa, an kama wanda ake zargin ne a lokacin da yake kokarin tserewa akan babur, inda ya kara da cewa an samu buhu a hannunsa dauke da kudi N4,986,000 da kuma bindigar AK-47 guda biyu tare da harsashi guda 47.

Advertisement

“A ranar 05/08/2024 da misalin karfe 02:00 na safe, wani mazaunin ƙauyen Yandadi dake karamar hukumar Kunchi ta jihar Kano ya kawo rahoton cewa wasu ‘yan fashi da makami sun dira gidan sa,inda suka yi masa fashin naira miliyan goma sha biyar (N15,000,000.00).

“Haka kuma duk a rana ɗaya da misalin karfe 06:00 na safe rundunar ta kama babban wanda ake zargi mai suna Hassan Iliya mai shekaru 35 a kauyen Alhazawa da ke karamar hukumar Musawa ta jihar Katsina a lokacin da yake kokarin tserewa a kan babur.

Advertisement

“A wani bincike da aka gudanar an gano wanda ake zargi ɗauke da buhua ciki akwai bindigu kirar AK-47 guda biyu dauke da harsashi guda 47 da kudi, wanda adadin ya kai naira miliyan hudu, da dari tara, da naira dubu tamanin da shida (N4,986,000.00)”, in ji Kiyawa.

A cigaba da jawabi Kakakin ya ci gaba da cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike yayin da yake kira ga jama’a da su guji aikata wani abu da zai iya haddasa tashin hankali, su kuma yi taka tsantsan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending