News
Hukumar NDPC Ta Ci Tarar Bankin Fidelity Naira Miliyan 555 800 000 Kan Bayanan Kwastomomi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar ƙare bayanan sirri ta Najeriya ta ci tarar Bankin Fidelity ƙasa da kashi ɗaya 0.1% cikin ƙudaden shigar da ta samu a bara, wato kwatankwacin dala 358,580 ko naira miliyan 555 800 000 saboda karya dokar bayanan kwastomomi da aka buɗewa asusun ajiya.
Hukumar ta NDPC ta shaida wa bankin Fidelity, mai matsakaicin matsayi a Najeriya, ya biya wannan tarar cikin kwanaki goma sha hudu masu zuwa saboda da wuce gona da iri wajen ƙarbar bayanan sirri masu ajiya a bankin ba bisa ka’ida bayan wani bincike da aka fara tun a watan Afrilun 2023.
Wannan ita ce tarar mafi girma da hukumar NDPC ta ci wani kamfani ko hukuma da ta karya dokar bayanan sirri, duk da cewa Fidelity na kalubalantar hukuncin.
A cikin wata sanarwa Bankin Fidelity, ya musanta saɓa duk wani ƙa’ida.
“A matsayinmu na banki, muna ci gaba da tattaunawa da NDPC kan yadda za a shawo kan lamarin.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
