Connect with us

News

Wata Mata Mai Shekaru 40 Ta Bankawa Kanta Wuta A Jigawa

Published

on

images 71

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

Wata mata mai suna Harira mai shekaru 40 ta yi nasarar Bankawa kanta wuta dalilin bakin cikin saki da mijinta ya yi mata a karamar hukumar Guri ta jihar Jigawa.

DSP Lawan Shiisu, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da aka fitar a garin Dutse, a yau Juma’a.

An Tsare Shugabannin Ƙananan Hukumomi 3 Kan Badaƙalar Naira Miliyan 660 A Kano

Jami’in ya bayyana cewa matar tana zaune ne a kauyen Garin Mallam,kuma ta ƙona kanta ne ta hanyar zubawa kanta man fetur daga bisani ta cinnawa kanta wuta.

“A ranar Alhamis ne muka sami labari mai ban tausayi inda rahoto ya iso mana cewar wata mata mai shekara 40 a kauyen Garin Mallam ta yayyafawa kanta fetur ta kuma cinnawa kanta wuta.

Haka kuma rahotanni sun bayyana cewa ta aikata wannan aika aika ne a bayan gari inda ba kowa.

Advertisement

Da samun wannan rahoto,nan take jami’an tsaro daga hedikwatar ’yan sanda ta Guri suka ɗunguma zuwa wurin da abin ya faru don sun tabbatar da faruwar lamarin.

“Nan take jami’an ƴan sanda su ka kai gawar zuwa asibiti, daga baya kuma suka mika ta ga yan uwan ta domin yi mata sutura,” in ji Shiisu.

Jami’in ya bayyana cewa binciken farko da aka yi ya nuna cewa marigayiyar ta kamu da cutar damuwa sakamakon bakin cikin da ta kunsa watanni baya saboda rabuwa da suka yi da mijin ta.

Haka kuma kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Ahmadu Abdullahi, bayya cewa ya kamata mutane su dinga neman shawara ko kuma su dawwama wa Ubangiji lamurran su.

Abdullahi ya kuma shawarci jama’a da su rika neman shawarwari da nasiha daga manya kan lamarin da suka shige musu duhu.

 

Advertisement

(NAN)

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending