Connect with us

News

Kusan Duka Ƴan Majalisun Najeriya Ƴan Ƙwaya Ne, Sannan Suna Fataucin Muggan Ƙwayoyi  —Sanata Sumaila

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

Sanata mai wakiltan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila, ya yi zargin cewa da yawa daga cikin ‘yan majalisar dokokin Najeriya na muamula da muggan kwayoyi musamman yayin da suke gudanar da ayyukansu.

Advertisement

Sumaila ya bayyana hakan ne a zaman majalisar na ranar Talata yayin da yake ba da gudummawa ga muhawara kan kudirin dokar kafa Cibiyar Wayar da kan mutane kan illolin shaye-shaye da gyara hali kamar yanda Jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito

Ba Na So Na Ce Uffan Game Da Rikicin Cikin Gida Da Ya Dabaibaye Jami’iyyar NNPP A  Kano —Kwankwaso 

Ya karaa da cewa kusan duka ƴan majalisa na muamula da kwayoyi. Sukan ajiye su a gundumomin su da gidajensu. Bayan haka ya zargi sanatocin da muamula da masu harkallar muggan kwayoyi a koda taushe.

Advertisement

” Bari in gaya muku yanzu haka da nake muku magana, kusan duka ofisoshinmu da gidajen mu duk danƙare suke sa kwayoyi tuli-tuli. Haka kuma a gidajenmu make suke da kwayoyi.

” Sannan kuma zan iya nuna muku wasu gaggan ƴan siyasa da ke mu’amala da masu harƙallar muggan kwayoyi. Saboda haka wannan magana dole mu maida hankali a kai.

Advertisement

Sanata Sumaila ya kara sa cewa “dole mu maida hankali bisa abinsa muka sa a gaba, mu ji tsoron Allah mu je a gwada mu kowa ya san matsayinsa.

Daga nan sai ya ƙalubalanci abokan aikinsa sanatoci, su rantse da Alkur’ani ko Bible cewa basu muamula da muggan kwayoyi da masu safara sa.

Advertisement

Haka sanata Sumaila ya cigaba da zargin sanatocin tana ƙalubalantarsu su rantse da Kur’ani ko Bible cewa basu kwankwaɗar kwayoyi.

Sai dai kuma kafin ya kammala jawabinsa, mataimakin shugaban majalisar wanda shine ya jagoranci zaman majalisan ranar Talata ya dakatar dashi.

Advertisement

” Sanata Sumaila, zan dakatar da kai, domin ka kauce daga ainihin abinda muke tattaunawa a kai. Ka koma ka zauna.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending