News
Yarinya ‘Yar Shekara 14 Ta Jagoranci Zaman Majalisar Dokoki A Jigawa
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
A jiya ne kakakin majalisar dokokin jihar Jigawa, Haruna Aliyu, ya karrama yarinyar a zauren majalisar ta hanyar raba kujerarsa ga ‘ya mace.
Wata yarinya ‘yar makaranta ‘yar shekara 14 mai suna Jamila Aliyu Abdulkadir, wacce ta gudanar da wani zama na musamman na tunawa da ranar ‘ya’ya mata ta duniya.
Ba Na So Na Ce Uffan Game Da Rikicin Cikin Gida Da Ya Dabaibaye Jami’iyyar NNPP A Kano —Kwankwaso
Sawaba Radiyo ta ruwaito cewa Ms Abdulkadir ta jagoranci zaman taron tare da wasu ‘yan mata ‘yan makaranta da suka fito daga makarantu daban-daban a Jigawa.
Ta tunatar da zauren majalisar cewa duk ‘yan mata na da hakkin samun rayuwa mai aminci, ingantaccen ilimi da ingantaccen salon rayuwa yayin da suka girma Jigawa.
Wata yarinya da ta wakilci karamar hukumar Dutse a wajen taron na musamman, Hassanah Aboyeji ta yabawa gwamnan bisa yadda ya ba da fifiko ga ilimin yara mata da kuma kokarin ganin ‘ya’ya mata sun samu ilimi kyauta a kowane mataki.
Esther Maiyaki, wacce ta wakilci mazabar jihar Buji a zauren taro na musamman, ta ce idan aka ba da dama ga ‘yan mata yadda ya kamata, za su iya taka muhimmiyar rawa a harkar kiwon lafiya a jihar, domin kashi 44 na al’ummar jihar mata ne.
Tun da farko, shugaban majalisar, Mista Aliyu, ya ce majalisar ta yi kokari sosai wajen karfafa mata da kuma sanya bege ga yarinyar. Ya ce jihar ta shirya tsaf domin magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta wanda ke zama kalubale a fadin kasar nan.
