Connect with us

News

Rundunar Yan Sanda Ta Kori Jami’an Ta 3 Saboda Kisan Dalibin Kwaleji

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Rundunar yan sandan jihar Kwara ta sanar da korar jami’an ta 3 bisa zargin su da taka rawa a kisan wani dalibin kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar a babban birnin jihar Ilorin mai suna Qoyum Abdulyekeen Ishola.

Advertisement

Lamarin kisan daya faru ranar 4 ga watan Satumba ya samu kalubalanta da yin ala wadai, wanda hakan yasa aka mayar da binciken kisan zuwa babban birnin tarayya Abuja, karkashin jagorancin shugaban yan sandan kasa Kayode Egbetokun.

Ɗalibi ɗan shekara 15 ya maka ma’aikatar ilimi, da JAMB da NUC a gaban kotu

 

Advertisement

Jami’an da aka kora sun hadar da Abiodun Kayode, Samuel da Oni Philip.

Jami’ar hulda da jama’a na rundunar DSP Toun Ejire-Adeyemi, tace an samu jami’an da laifukan da suka shafi cin hanci da Kuma yin amfani da karfi a inda bai kamata ba.

Advertisement

Tace nan gaba kadan za’a gurfanar da jami’an da aka kora.

Daily Trust ta ruwaito cewa an kashe dalibin lokacin zanga zangar karin farashin man fetur

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending