Connect with us

News

Ɗalibi ɗan shekara 15 ya maka ma’aikatar ilimi, da JAMB da NUC a gaban kotu

Published

on

Ambaliyar RuwaZulum Ya Rufe Ɗauƙacin Makarantun Firamare Da Ke Jihar Nan Take

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Master Chinaemere Opara ya maka ma’aikatar ilimi ta tarayya da hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa (JAMB) da kuma hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) a gaban kotu a kan sabon tsarin gwamnati na hana wadanda basu kai shekaru 18 shiga jami’a ba.

Opara, dalibi dan shekara 15 kuma dan makarantar sakandare, ya shigar da karar ne ta hannun baffansa, Mista Maxwell Opara da mahaifinsa da kuma lauya, a babbar kotun tarayya dake Abuja, a jiya Litinin.

Kotu Ta Daure Magidanci Da Matarsa Da ’Ya’yansu Biyar Kan Shiga Gidan Surukinsu

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya bayar da rahoton cewa, a cikin karar da aka shigar, mai lamba: FHC/ABJ/CS/1512/2024 mai kwanan wata 30 ga Satumba da kuma ranar 14 ga Oktoba Wayne Elijah ya shigar da karar, dalibin dan aji biyar a sakandare, wacce ma’aikatar, JAMB da NUC a matsayin waɗanda ake kara na 1 zuwa 3 bi da bi.

A cikin korafe-korafen nasa guda shida, mai ƙarar ya nemi a bayyana cewa takaita shekarun shiga jami’a ya nuna wariya kuma baya cikin kundin tsarin mulki na ƙasa.

Ya ce hakan ya zama take ƴancin fadin albarkacin baki kamar yadda sashe na 42 na kundin tsarin mulkin 1999, 2011 (kamar yadda aka gyara) da kuma sashi na 2, 3, 4, 5, 10, 13 (2), 17 da 28 suka tabbatar na Yarjejeniyar Afirka Kan Hakkokin Dan Adam da Jama’a.

Advertisement

Ya bukaci kotun da ta bayyana cewa waɗanda ake kara basu da ikon take hakkin sa na rayuwa a kasar.

 

 

 

DAILY NIGERIAN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending