News
Ba Wanda Ya Isa Yace Mana Ga Yadda Zamu Sarrafa Kudadenmu Da Amurka Ta Dagewa Takunkumi – Iran
Gwamnatin Iran ta bayyana cewa ita kaɗai ce ke da ikon yanke shawarar yadda za ta sarrafa kuɗaɗen da za a sake mata bayan Amurka ta amince da sassauta wasu takunkuman tattalin arziki da aka ƙaƙaba mata.
Wannan martani ya biyo bayan kalaman Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya ce duk wasu kuɗaɗen Iran da za a saki za a adana su ne a wani asusu na musamman da ke ƙarƙashin kulawar gwamnatin Amurka.
IGP Disu Ya Haramta Wa Jami’an ’Ƴansanda Yin Harkoki A Soshiyal Midiya Ba Tare Da Izini Ba
A cewar Trump, Iran za ta iya amfani da waɗannan kuɗaɗe ne kawai wajen sayen kayan abinci da magunguna, kuma za a gudanar da sayayyar ne daga Amurka.
Sai dai Iran ta yi watsi da wannan sharaɗi, tana mai cewa babu wata ƙasa da ke da hurumin sanya mata yadda za ta tafiyar da kadarorinta ko kuma yadda za ta kashe kuɗaɗenta.
Jakadan Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Geneva, Ali Bahreini, ya jaddada cewa gwamnatin Iran ce kaɗai ke da ikon tsara yadda za ta yi amfani da kuɗaɗen da za a sake mata.
Bahreini ya ce, “Iran ce kaɗai za ta yanke shawara kan yadda za ta sarrafa kadarorinta. Babu wata ƙasa da za ta gaya mana yadda za mu kashe kuɗaɗenmu.”
Tun da farko ma, Tehran ta yi fatali da irin waɗannan sharuɗɗa da mataimakin shugaban Amurka, J. D. Vance, ya gabatar yayin tattaunawar sasanci da aka gudanar a ƙasar Switzerland.
Lamarin na nuna yadda har yanzu ake ci gaba da samun sabani tsakanin Iran da Amurka kan yadda za a aiwatar da yarjejeniyoyin da suka shafi sassauta takunkumin tattalin arziki da kuma amfani da kuɗaɗen Iran da aka daskarar a ƙasashen waje.
