News
Babu Ɗalibin Da Zai Bar Makaranta Saboda Rashin Kuɗi A Mulkina – Shugaba Tinubu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, ya lashi takobin cewa a mulkinsa, babu ɗalibin da zai bar makaranta bai kammala ba saboda kawai ba zai iya biyan kudin makaranta ba.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a bikin yaye dalibai karo na 33 da Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Akure a Jihar Ondo ta shirya ranar Asabar.
Tinubu, wanda tsohon shugaban Kwalejin Lafiya ta Afirka ta Yamma, Farfesa King-David Terna Yawe, ya wakilta, ya bukaci kungiyoyi daban-daban na manyan makarantu da su hada kai da gwamnati domin tabbatar da zaman lafiya a cikin makarantun.
Game da shirin gwamnatinsa na ba ɗalibai rance kuwa, Tinubu ya ce, “Wannan shiri zai ba dukkan dalibai masu karamin karfi damar karbar bashi mara ruwa, wanda za su iya biya daga baya, idan suka fara aiki.
“Matukar ina mulki, kamar yadda na fada a kundin manufofina, babu wani dalibi da zai bar makaranta saboda rashin kuɗi.
“Gwamnatina ba za ta yi wasa da nauyin da ya rataya a wuyanta ba a wannan bangaren. Za mu tabbatar dukkan manyan makarantu sun sami kudadensu saboda su yi ayyukansu yadda ya kamata,” in ji Tinubu.
Sai dai Shugaban ya shawarci kungiyoyin ma’aikatan manyan makarantu da su rungumi hanyoyin tattaunawa na ruwan sanyi a maimakon a kodayaushe su rika tsunduma yajin aiki, matakin da ya ce yana gurgunta tsarin ilimi a kasar nan
A wani labarin kuma Boko Haram Sun Raunata Jami’an Tsaron Gwamnan Jihar Yobe 6
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
