Politics
Ba Na So Na Ce Uffan Game Da Rikicin Cikin Gida Da Ya Dabaibaye Jami’iyyar NNPP A Kano —Kwankwaso
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Dan takarar shugabancin Nijeriya karkashin jami’iyyar NNPP a zaben da ya gabata na shekarar 2023 Engr Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ya yanke shawarar ba zai ce komai ba game da rikicin cikin gida da ya dabaibaye jami’iyyar NNPP a jihar Kano.
Kwankwaso na magana ne a gidansa na Miller Road a ranar Talata, a lokacin da wani dan jarida ya tambaye shi kan rikicin da ya mamaye jami’iyyar NNPP, ya ce shi ba ya da abin cewa kan wannan batu kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Rundunar Yan Sanda Ta Kori Jami’an Ta 3 Saboda Kisan Dalibin Kwaleji
Advertisements
