Arziƙin Aliko Dangote ya ninka ne zuwa dala biliyan 28 bayan matatar man da ya gina ta fara aiki a watan Satumba, kamar yadda mujallar Bloomberg ta bayyana.
A watan da ya gabata ne Dangote ya shaida wa BBC cewa matatarsa tana iya samar da fiye da man da ake buƙata a Najeriya.