Connect with us

Opinion

Duk Wanda Allah Yayi Wa Wata Baiwa Ko Daukaka To Sai Ya Hadu Da Sharrin Mahassada

Published

on

FB IMG 1730373107800
Spread the love

 

 

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Advertisement

Assalamu alaikum

Ya ku ‘yan uwa masu albarka! Tabbas, hakika, ko shakka babu, duk wanda Allah Subhanahu wa Ta’ala yayi wa wata daukaka, ko wata baiwa, ko wata ni’ima, ko wace iri ce, to ya sani, lallai sai yayi hakuri, domin makiya, da mahassada sai sun sa shi a gaba.

Dole za’a nuna masa kiyayya a fili karara, ban da sharri da makirci da kulle-kullen da suke kullawa a boye, wanda shi bai sani ba.

Advertisement

Ko shakka babu, idan ka ga ba’a yi maka hassada, to ka sani cewa kai ba kowa bane a cikin al’ummah, ko kuma ba ka da komai. Amma matukar kai wani ne. Matukar Allah yayi maka wata baiwa ko daraja ko daukaka, to kace ma ba za’a yi hassadar ka ba wannan ma bai taso ba.

Kuma ka sani, masu yi maka hassadar nan, wallahi ko wace hanya daga cikin hanyoyi, zasu iya bi domin ganin sun cimma burin su. Wato ko dai ni’imar ta gushe, ko kuma su nemi halakar da kai baki daya, domin a ganin su, haka ne kawai zai sa su huta, kuma su huta daga bakin ciki da suke ciki, na kallon ka a koda yaushe, cikin ni’imar da Allah Subhanahu wa Ta’ala yayi maka.

Kuma kar ka dauka cewa kai kafi karfin ayi maka hassada. Don Allah ina Annabin Allah, Muhammad (SAW)? Shin ba ayi masa hassada ba? Bai hadu da sharri da makircin Mahassada ba? Ina Annabin Allah Yusuf? Shin ‘yan uwansa basu yi masa hassada ba, har suka nemi su hallakar da shi? Ina ‘ya ‘yan Annabin Allah Adam, daya bai kashe daya saboda cutar hassada ba?

Advertisement

Don haka, kar ka dauka cewa kai ka tsallake sharrin su, kar ka cika baki game da sharrin mahassada. Dan uwa, kai dai yi kokari ka nemi tsarin Allah da kariyar sa, akan sharrin hassada da mahassada. Wannan shine kawai mafita. Allah ya kare mu baki daya, amin.

Ayoyin Alkur’ani mai girma masu tarin yawa, da Hadisan Manzon Allah (SAW) masu yawa, sun yi muna bayanin cutar hassada da maganinta. To anan ba sai na kawo dukkanin su ba, amma ga wani Hadisin Manzon Allah (SAW), da yake tabbatar da cewa, duk wanda Allah yayiwa daukaka to tabbas sai yayi karon batta da mahassada:

عن معاذ بن جبل قال، قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:

Advertisement

“استعينوا على قضاء حوائجكم بالكتمان فإن كل ذي نعمة محسود.”

Ma’ana:

Daga Mu’azu Dan Jabal yace, Manzon Allah (SAW) yace:

Advertisement

“Ku nemi taimakon Allah wurin biyan bukatun ku ta hanyar boye sirrin ku, domin ko wane mutum ma’abuci ni’ima abun yiwa hassada ne.”

Wannan hadisi wasu daga cikin malamai sun raunana shi, amma a hakikanin gaskiya, hadisi ne ingantacce. Babban malamin hadisi, Sheikh Muhammad Nasiruddin Al-Albani ya inganta shi a cikin littafin sa mai albarka, wato Silsilatu Ahadisis-Sahiha, mujalladi na 3, shafi na 436, lambar hadisi na 1,453, da kuma dayan littafinsa mai suna Sahihul Jami’, lambar Hadisi na 943.

Sheikh Al-Albani ya kawo dukkanin maganganun malaman da suka raunata Hadisin, amma dai daga karshe ya inganta shi daga ruwayar Sahal Dan Abdur-Rahman Al-jurjaniy, daga Muhammad Dan Mudarraf, daga Muhammad Dan Munkadir, daga Urwata Dan Zubair, daga Abu Hurairah, kuma Hadisi ne Marfu’i. Sheikh Muhammad Nasiruddin Al-Albani yace, wannan Hadisi ta wannan isnadi, Hadisi ne mai kyau. Domin karin bayani ka dubi As-Sahiha, mujalladi na 3, shafi na 439.

Advertisement

‘Yan uwa masu girma! Hassada ita ce jin zafi, ko jin haushi, ko nuna damuwa, ko kiyayyar wani abu ko wata baiwa, ko daukaka ko daraja da wani yake da ita. Ko kuma ace buri ko fatan gushewa ko lalacewar wata ni’ima ko baiwa ko daukaka da Allah ya ba wani.

Hassada ita ce ganin kyashi, nunkufurci, kiyayya. Wanda ake yiwa hassada shine wani mai abun hannu ko mai wani matsayi na addini ko na duniya, ko wani mukami. Abin da yasa marasa imani suke yin hassada shine, rashin kyakkyawan tunani, izza, ji-ji-da-kai, son girma, son daukaka, son shugabanci ko isa, ko kazantar zuciya, ko mugunta, ko zalunci ko mummunar dabi’a. Ina addu’a da rokon Allah Ya tsare dukkan Musulmin kirki daga sharrin hassada, amin.

Hassada ita ce mutum yayi burin abin da yake wajen wanda ake yiwa hassadar na alheri, na abin duniya ne ko na addini, ya gushe. Wannan dukkanin malamai sun tafi akan haramun ne, domin Allah da Manzonsa (SAW) sun hana, kuma yana cutar da jiki da addini.

Advertisement

Dan uwa mai daraja! Idan kana tsoron cutarwa daga wani mutum ko wani mahassadi, ko wasu mahassada, ko kana fuskantar cin mutunci ko tsana ko kiyayya ko hassada daga gare shi, ko daga wata jama’arsa, to ga addu’ar da zaka rinka karantawa domin samun kariya daga wurin Allah Subhanahu wa Ta’ala akan duk wani sharri da makirci nasa. Kuma idan ka rike wannan addu’a kana yi, kuma ‘yan uwa bayin Allah suna taimaka maka da addu’o’i, to da izinin Allah aniyarsu zata koma kansu, in Allah yaso. Kuma zaka ambaci sunansa karara a cikin addu’ar. Ga addu’ar nan kamar haka:

“اللَّهُمَّ رَبَّ السَّمَاوَاتِ السَّبْعِ، وَرَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ، كُنْ لِي جَاراً مِنْ (اِسمُه) وَأَحْزَابِهِ مِنْ خَلاَئِقِكَ، أَن يَفْرُطَ عَلَيَّ أَحَدٌ مِنْهُمْ أَوْ يَطْغَى، عَزَّ جَارُكَ وَجَلَّ ثَنَائُكَ، وَلَا إِلَهَ إِلَّا أَنْت.”

“Allahummah, Rabbas-samawatis-sab’i, wa Rabbal-Arshil-Azim, kun li jaran min (Sai ka ambaci sunansa), wa ahzabihi min khala’iqika, an yafruta alayya ahadun minhum aw yatgha. Azza jaruka, wajalla thana’uka, wa la ‘ilaha ‘illa Anta.”

Advertisement

Ma’ana:

“Ya Allah, Ya Ubangijin Sammai bakwai! Ya Ubangijin Al’arshi mai girma! Ina rokonka, Ka zama Mafaka a gare ni daga sharrin wane (Sai ka ambaci sunansa) da shi da jama’arsa daga cikin halittunka. Kada wani daga cikinsu yaci mutunci na, ko yayi wata cutarwa a gare ni. Mafakarka ta buwaya, kuma yabonka ya daukaka. Kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Kai.”

Sannan yana daga cikin kariyar Allah daga sharrin su, ka yawaita karanta Falaki da Nasi, domin suna da muhimmanci kwarai da gaske. Manzon Allah (SAW) yace:

Advertisement

“Ba’a taba yin wata addu’a ta neman tsari kamar su ba.”

Kuma shi kansa Manzon Allah (SAW), ya kasance a da can yana yin wasu addu’o’in neman tsari. Amma tun da aka saukar masa da falaki da nasi, sai ya kyale komai ya rike su. Har ma ya kan karanta su ya tofa a hannayen sa, sannan ya shafe jikin sa da su.

Sannan ana bukatar yawan karanta Ayatul Kursiyyu. Ayatul kursiyyu ita ce aya mafi girma a cikin littafi mafi girma wato Alkur’ani. Kuma ita ce ayar da shaidan da kansa ya bada shaida game da muhimmancinta. Yazo a cikin hadisi, Annabi (SAW) yace:

Advertisement

“Idan ka tafi zuwa wurin kwanciyar ka, ka karanta Ayatul Kursiyyu. Tun daga farkon ta har zuwa karshen ta. To hakika ba zaka gushe ba, kana da mai tsaro na musamman daga wurin Allah. Kuma babu wani shaidanin da zai kusance ka har gari ya waye.” [Bukhari ne ya fitar da hadisin]

Sannan ka rinka yawaita karatun Alkur’ani a gidan ka, ko kasa a rinka yawan karanta maka shi, musamman yawan karanta Suratul Bakara. Saboda hadisin da Manzon Allah (SAW) yake cewa:

“Kar ku mayar da gidajen ku kamar makabartu. Domin hakika shaidan ba ya kusantar gidan da ake karanta Suratul Bakara.” [Bukhari da Muslim ne suka fitar da shi]

Advertisement

Kuma ita wannan cutar Hassada, a yau ta kusa ta mamaye dukkan al’ummah. Sannan zaka same ta a cikin ko wane irin jinsi na mutane. Ba’a kebe wasu mutane ba, wadanda za’ace a cikin su ne kadai ake samun cutar Hassada ba. Don haka zaka iya samun Hassada tsakanin malamai, zaka iya samun Hassada tsakanin sarakuna, zaka iya samun Hassada tsakanin masu kudi, zaka iya samun Hassada tsakanin ‘yan kasuwa, zaka iya samun Hassada tsakanin ma’aikatan gwamnati, zaka iya samun Hassada tsakanin jami’an tsaro, zaka iya samun Hassada ko’ina, kai hatta ma a cikin ‘yan uwa ana samun ta. Don haka a ko’ina akwai cutar Hassada.

Idan kaga babu Hassada, to babu samun ci gaba, ko samun daukaka, ko samun wata baiwa ko ni’ima.

Ya ku ‘yan uwa! Wallahi kar muyi wasa da sharrin Mahassada. Miyagu ne su a cikin al’ummah. Ka sani, mai yi maka hassada, wallahi ba ya shakkar ya bi ko wace irin hanya, domin ya cutar da kai. Domin shi ci gaban ka ne baya so gaba daya. Daukakar da Allah yayi maka ne yake adawa da ita. Da zaka mutu yau, to shi da bukatar sa ta biya kenan. Da zaka lalace, da zaka wulakanta, da zaka tozarta, to shi da burinsa ya cika, kuma abunda yake nema ya samu. Don haka kar kayi wasa, ka nemi taimakon Allah da tsarin sa daga sharrin dukkan wani mai hassada idan yayi hassadar.

Advertisement

Dan uwa, idan kayi wasa da addu’a, to lallai zaka hadu da kalubale mai girma.

Allah ya tsare mu, amin.

Wassalamu alaikum,

Advertisement

Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuta, daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samunsa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *