News
Tsofaffin Sojoji sun rufe ma’aikatar kudi Ta Abuja Sakamakon Rashin Biyansu Hakkunansu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsofaffin sojojin karkashin kungiyar Coalition of Military Pensioners sun rufe Ma’aikatar Kudi ta Abuja da safiyar Alhamis saboda rashin biyan karin albashi daga kashi 20% zuwa 28% daga watan Janairu zuwa Nuwamba 2024.
Jami’an sojojin da suka zo daga sassa daban-daban sun nuna takaicinsu game da gazawar Gwamnatin Tarayya a wajen biyansu hakkokinsu.
Tsofaffin Sojoji sun rufe ma’aikatar kudi Ta Abuja Sakamakon Rashin Biyansu Hakkunansu
DAILY NIGERIAN HAUSA ta rawaito cewa a cikin Bukatun da suka nema sun hada da biyan su kudin daga Oktoba 2023 zuwa Nuwamba 2024 da kuma Biyan karin N32,000 ga fanshon su.
Biyan kudin Security Debarment Allowance (SDA) gaba daya.
Dawowar kudaden da aka cire daga fanshon sojojin da aka sauke saboda rashin lafiya, da sauransu.
