News
Ya Kamata Mawadata Da Kuma Kungiyoyi Su Dinga Taimaka Wadanda Aka Daure A Gidan Ajiya Da Gyaran Hali — Hajiya Azumi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugabar kwamitin yiwa daurarru afuwa a jihar Kano hajiya Azumi Namadi Bebeji ta bukaci al’umma musammam mawadata da kuma ‘yan kungiyoyin cigaban al’umma da su dinga taimaka wadanda aka daure a gidajen a gidan ajiya da gyaran hali a fadin jihar Kano.
Hajiya Azumi ta baiyyana hakan ne a yayin zantawar ta da manema labarai. Sakamakon ban kwana da shekarar 2024.
Zarge-zargen da gwamnatin mulkin sojin Nijar ke yi wa Najeriya ba su da tushe balle makama
Ta ce gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf na sane da daurarrun kasancewar akwai tanade-tanade da ya ke yi masu.
Ta kuma yabawa gwamnan da mataimakin sa, kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo bisa yadda su ke gabatar da ayyukan alheri ga al’ummar
jihar.
Advertisements
