News
Innalilahi Wainailahi Raju,un: Gwamnan Jigawa ya sake rasa dansa awanni bayan rasuwar mahaifiyarsa.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya sake rasa dansa Abduwahabu, kasa da awanni 24 bayan rasuwar mahaifiyarsa.
Sakataren yada labaran gwamnan Hamisu Mohammed Gumel ne ya sanar da rasuwar.
Ya ce Abdulwahabu ya rasu yana da shekaru 24, biyo bayan hatsarin mota da ya rutsa da shi a kan titin Dutse zuwa Kafin Hausa a ranar Alhamis.
Tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Advertisements
