News
Jami’an Hukumar NAFDAC Ta Lalata Kayayyakin Jabu Da Abinci Na Sama Da Naira Biliyan 120
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar NAFDAC ta yi nasarar lalata magunguna, kayan abinci, da kayan sha na jabu da suka kai darajar sama da Naira biliyan 120 tsakanin Oktoba zuwa Disamba 2024.
Shugabar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta ce za a dauki mataki mai tsauri kan masu kawo hadari ga lafiyar ‘yan kasa ta hanyar rarraba kayan jabu.
Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Amince Da Naira Dubu 70 A Matsayin Mafi Karancin Albashi
NAFDAC ta kai samame a kasuwanni da manyan shaguna a jihohi da dama, ciki har da Legas, Abuja, Kaduna, da Aba.
Hukumar ta lalata magunguna marasa rajista na Naira biliyan 11 a Ibadan da shinkafar jabu ta Naira biliyan 5 a Abuja da Nasarawa.
Farfesa Adeyeye ta gargadi jama’a da su rika siyan kayan da ke da lambar rajista ta NAFDAC daga wuraren da ake iya gane su, tana mai tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da kawar da kayayyakin da za su iya cutar da lafiyar al’umma.
-
News6 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News6 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
