News
Tsohon Kwamishinan Yada Labarai Na Kano Dan tiye Ya Kai Ziyarar Taya Murna Ga Sabon Kwamishina Waiya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Advertisements
Advertisements
Tsohon kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Hon. Baba Halilu Dantiye, ya kai ziyarar taya murna ga magajinsa, Comr. Ibrahim Abdullahi Waiya, domin taya shi murnar nadin da aka yi masa kwanan nan .
Advertisements
Comr. Waiya ta tarbi Hon. Halilu Dantiye, ya nuna matukar godiya ga wannan karimcin. Ya kuma yabawa Baba Halilu Dantiye a matsayinsa na “mai kirki kuma mai tawakkali” tare da jinjinawa dimbin gudunmawr da ya bayar da kuma abubuwan da ya bari a baya.
Advertisements
Advertisements
“Na yaba da irin sadaukarwar da kuke yiwa jihar Kano,” inji Comr. Waiya .
Comr. Waiya ya yiwa Hon. Halilu Dantiye da fatan alheri a cikin ayyukansa na gaba, tare da yaba gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban jihar.
Advertisements
