Connect with us

News

Kotun daukaka Kara Ta Ce Kotun Tarayya Ba Ta Da Hurumin Shiga Dambarwar Masarautar Kano

Published

on

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta ce Kotun Tarayya ba ta da hurumin shiga Dambarwar Masarautar Kano.

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamnta a Abuja ta bayar da umarnin sake sauraron shari’a kan rikicin masarautar Kano da ya haɗa da Alhaji Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi.

Kotun ɗaukaka ƙara da ta yanke a yau, ta ce ba’a yi wa Sanusi adalci ba saboda yadda wata babbar kotun Kano ta gudanar da shari’a a kansa.

Tsohon Kwamishinan Yada Labarai Na Kano Dan tiye Ya Kai Ziyarar Taya Murna Ga Sabon Kwamishina Waiya

Mai shari’a Mohammed Mustapha wanda ya yanke hukuncin, ya bayyana cewa babbar kotun Kano ba ta yi wa Sanusi adalci ba ta hanyar gudanar da shari’a ba tare da bashi damar bayanin nasa bangaren ba.

Saboda haka ne kotun ɗaukaka ƙara ta bayar da umarnin a mika karar ga babban alkalin alkalai na jihar Kano domin baiwa wani alkali damar yanke hukuncin adalci cikin gaggawa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending