News
Majalisar Dattijai Ta Naɗa Sanata Babangida Hussaini a Matsayin Ciyaman na Kwamitin NWDC
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da naɗin Sanata Babangida Hussaini (Walin Kazaure), mai wakiltar Jigawa North West, a matsayin Ciyaman na Kwamitin Majalisar Dattawa na Hukumar Cigaban Arewa Maso Yamma (North West Development Commission – NWDC).
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya sanar da wannan naɗi yayin zaman Majalisar a safiyar Talata.
Al’ummar Rimin Zakara Sun Gudanar Da Alqunut Domin Neman Diyyar Gonaki Da Gidajensu
Kafin wannan sabon muƙami, Sanata Babangida Hussaini ya kasance Ciyaman na Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da Hukumar Titunan Tarayya (FERMA). Haka kuma, ya taɓa riƙe mukamin Babban Sakataren Ma’aikatar Tsaro da Ma’aikatar Ayyuka ta Ƙasa, inda ya bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen cigaban ayyukan gwamnati.
Hukumar NWDC dai wata cibiya ce da aka kafa bisa doka bayan da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya gabatar da ƙudurin kafata a gaban Majalisar. Hukumar za ta gudanar da ayyukan ta a jihohi bakwai na Arewa Maso Yamma, tare da hedikwatarta a Jihar Kano.
Wannan mataki na nuna ƙudirin Majalisar Dattawa na tabbatar da ci gaban yankin Arewa Maso Yamma da samar da ingantattun ayyuka ga al’ummarta.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
