News
Daliban Jami’ar Northwest Sun Kai Gudummawa Gidan Gyaran Hali A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A wani yunkuri na tallafawa al’umma, wasu daliban da suka kammala karatun su a fannin Ilimin Kimiyyar Bayanai da Dakin Adana Bayanai (Library and Information Science) a Jami’ar Northwest, Kano, sun kai gudummawar kayan bukatun yau da kullum zuwa Gidan Gyaran Hali da Tarbiyya na Kurmawa, Kano.
Ziyarar ta gudana ne karkashin jagorancin Kwamared Abdurrashid B. Imam, tare da wasu daga cikin abokan karatu, inda suka bayyana cewa manufar wannan aiki shi ne tallafawa wadanda ke tsare a gidan gyaran hali, tare da tunatar da al’umma muhimmancin taimakon marasa galihu.
Majalisar Dattijai Ta Naɗa Sanata Babangida Hussaini a Matsayin Ciyaman na Kwamitin NWDC
A cewar B. Imam, “Mun sake lekawa gidan gyaran halin ne domin kara bada gudummawar mu ga waɗanda suke rayuwa a wancan gida.”
Har ila yau, ya yi kira ga daidaikun al’umma, kungiyoyin dalibai, da kungiyoyin da ba na gwamnati ba da su ci gaba da tallafawa waɗanda ke killace a gidajen gyaran hali domin ba su damar inganta rayuwarsu.
A karshe, shugaban tawagar ya mika godiya ga dukkan wadanda suka bada gudummawa, wanda hakan ya ba su damar aiwatar da wannan aikin alkhairi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
