Connect with us

News

Ribadu Ya Nemi Naja’atu Ta Janye Kalaman Zargi Kansa Ko Su Wanye A Kotu

Published

on

Tinubu ya saka hannu kan kudirin kafa cibiyar hana yaɗuwar ƙananan makamai ba bisa ƙa’ida ba – Ribaɗu

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Mai bai wa Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, NSA, Nuhu Ribadu, ya nemi Naja’atu Muhammad ta janye sannan ta kuma ba shi hakuri bisa wani bidiyon TikTok da ya karaɗe shafukan yanar gizo, inda ta zargi Ribaɗu da yin amai da lashewa.

Advertisement

DAILY TRUST da wasu jaridu sun buga cewa a cikin bidiyon TikTok ɗin, Naja’atu ta zargi Ribadu da yin aiki a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, bayan ya soke shi sau da dama a lokacin da ya ke Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) a baya, suka irin na zargin babakere da kuɗaɗe.

Daliban Jami’ar Northwest Sun Kai Gudummawa Gidan Gyaran Hali A  Kano

A cikin wata wasiƙa ta hannun lauyansa, Ahmed Raji, Ribadu ya bayyana cewa, a fili ko a sirrance, bai taɓa sukar Tinubu ba a lokacin da ya ke shugabantar EFCC.

Advertisement

A bidiyon dai an ji Naja’atu na zargin cewa, Ribadu ya bayyana Tinubu a matsayin Gwamnan da ke kan gaba wajen cin hanci a lokacin da ya ke gwamnan Legas shi kuma Ribadu ke rike da shugabancin EFCC.

Ribaɗu ya ce bai taɓa ko da sau ɗaya ba suka, tsakala ko tona wani zargin kan almundaha a lokacin Tinubu na gwamnan Legas.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending