News
Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Ƙarar Fubara Kan Shugabancin Majalisar Dokokin Ribas
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Wani kwamitin alkalai biyar na Kotun Koli ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Uwani Abba-Aji ta yi watsi da ƙarar da Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya shigar yana kalubalantar shugabancin Majalisar Dokokin Jihar Ribas ƙarƙashin jagorancin Martin Amaewhule.
Mai shari’a Uwani Abba-Aji, yayin da yake yin watsi da ƙarar, ya kuma yanke hukuncin cewa Fubara zai biya naira miliyan biyu ga Majalisar Dokokin Jihar Ribas .
Watsi da ƙarar da Fubara ya shigar ya biyo bayan janyewar shari’ar da lauyansa, Yusuf Ali, ya yi.
Advertisements
