News
Fubara Ya Musanta Zargin Yana Da Hannu A Hare-haren Da Ake Kai Wa Bututun Mai
Dakataccen gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya musanta zargin da gwamnatin tarayya ke masa na cewa yana da hannu a hare-haren da ake kai wa bututun mai a yankin Neja-Delta.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Nelson Chukwudi, ya fitar, Fubara ya bayyana cewa an alaƙanta shi da lamarin ne kawai saboda rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar, wanda ya kai ga dakatar da shi daga kujerarsa.
A halin yanzu, hare-haren kan bututun mai na janyo asarar miliyoyin daloli ga Najeriya, tare da haifar da barazana ga tattalin arzikin ƙasa.
Wannan lamari na zuwa ne yayin da ake ci gaba da sukar kafa dokar ta ɓaci a jihar, matakin da majalisun ƙasa suka amince da shi domin shawo kan rikicin.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News1 day ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
