News
An Kama Jarkokin Manja Cike Da Alburusai 488 A Abuja
Rundunar ‘yan sandan Birnin Tarayya Abuja ta cafke wani mutum ɗauke da harsashi 488 na bindigogin AK-47 da aka ɓoye a cikin jarkokin manja a tashar mota.
Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda mai kula da sintiri na musamman a Abuja, DCP Ishaku Sharu, ya bayyana hakan yayin da aka holen wanda ake zargin a ofishin rundunar a ranar Litinin.
Tsoffin Daliban Makarantar CAS Ta Kano Sun Tallafawa Marayun Abokan Karatunsu Da Naira Miliyan 2.8
Ya ce binciken farko ya nuna cewa wani mutum mai suna Yakubu Kacalla daga Funtua, Jihar Katsina, ya biya wanda ake zargin N100,000 domin karɓo masa makaman daga Jihar Nasarawa kamar yanda Jaridar AMINIYA ta ruwaito
Jami’an ƙungiyar masu sufurin motocin haya (NURTW) ne suka taimaka wajen kama wanda ake zargin, wanda asali mazaunin Jihar Katsina ne.
A halin yanzu, ‘yan sanda na ci gaba da bincike domin gano sauran masu hannu a safarar makaman.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News1 day ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
