Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Wa’adin Tantance Ma’aikata

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bai wa duk ma’aikatan gwamnatin tarayya wa’adin ranar Litinin, 17 ga Fabrairu, 2025, domin tantance sahihancin bayanansu a shirin kawar da ma’aikatan bogi.

A cikin wata sanarwa daga Ofishin Akanta-Janar na Tarayya, an bayyana cewa ma’aikatan za su yi rijista ta shafin IPPIS, tare da samar da TIN, lambar IPPIS, da lambar asusun albashi domin tabbatar da ingancin tsarin biyan albashi.

Iyaye Sun Fara Bibiyar ‘Ya’yansu a Shafukan Sada Zumunta: Shin Wannan Mataki Zai Rage Yada Barna?

Sanarwar ta kuma nuna cewa an ƙara wa’adin tantance bayanan albashi har zuwa ranar 17 ga Fabrairu, 2025, domin bai wa waɗanda ba su kammala ba damar yin hakan. Gwamnati ta ja kunne cewa duk wanda ya kasa kammala rijistar kafin ƙarfe 12 na dare a wannan rana, za a iya dakatar da albashinsa.

 

Wannan mataki na daga cikin yunkurin da Shugaba Bola Tinubu ya fara tun shekarar 2024, inda ya umarci cewa duk ma’aikatan da ke karɓar albashin gwamnati bayan komawa ƙasashen waje su mayar da kuɗaɗen da suka karɓa, tare da hukunta shugabanninsu da suka rufe ido kan wannan badaƙala.

Advertisement

Gwamnati na ci gaba da yin kira ga ma’aikatan gwamnati da su gaggauta cika sharuddan da aka gindaya domin kauce wa fuskantar hukunci.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending