Connect with us

News

Yadda Faɗuwar Farashin Gas Din Girki A Kano Ya Jawo Dogon Layi A Lokacin Azumi

Published

on

Spread the love

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

A daidai lokacin da al’ummar Musulmi suka fara azumin watan Ramadana, an wayi gari da cinkoson jama’a a gidajen sayar da iskar gas a birnin Kano, bayan sauƙin farashin da aka samu.

Gidajen sayar da iskar gas kamar Ultimate Gas da AA Rano da ke Sabuwar Gandu sun cika makil da jama’a, inda mutane ke tururuwar sayen gas domin girki a lokacin azumi.

Gobara Ta Kone Wasu Shaguna a Kasuwar Kofar Wambai Dake Birnin Kanon Dabo

Binciken PREMIUM TIMES ya gano cewa sauƙin farashin gas ne ya jawo farin ciki a tsakanin al’umma. A baya, ana sayar da kilogiram ɗaya na gas da kusan N1,500 zuwa N1,600, amma yanzu farashin ya sauka zuwa N1,160.

Advertisement

Wannan ragi ya sa mutane da dama suka koma amfani da gas maimakon gawayi, musamman a lokacin azumi da ake bukatar girki cikin sauri.

A watan Oktobar 2024, ƙaramin ministan man fetur, Ekperikpe Ekpo, ya ba da umarnin daina fitar da iskar gas na girki zuwa ƙasashen waje domin rage tsadar farashi.

Yanzu, alamu na nuna cewa matakin da gwamnati ta ɗauka yana haifar da sakamako, kuma kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu.

Yayin da farashin iskar gas ke sauka, al’umma na fatan cewa sauƙin farashin zai dore, musamman a wannan lokaci na azumi da ake bukatar girki cikin gaggawa.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *