News
Hukumar Sufurin Jiragen Ruwa Za Ta Haɗa Kai Da NDLEA Don Gwajin Ƙwaya Ga Matukan Kwale-Kwale
Hukumar kula da sufurin jiragen ruwa a Najeriya ta bayyana cewa za ta yi aiki tare da Hukumar Yaki da Sha da Safarar Ƙwayoyi ta NDLEA domin yin gwajin ƙwaya ga matukan kwale-kwalen da ke jigilar mutane a Jihar Neja.
Manajan shiyyar, Akapo Adeboye, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar, wanda ya samu halartar ‘yan kasuwa da manoma a Karamar Hukumar Katcha.
An Kullewa Gwamna Fubara shiga Kofar Majalisar Dokokin Ribas
Jihar Neja na daga cikin yankunan da ke fuskantar yawan hadurran kwale-kwale, wanda ke haddasa asarar rayuka da dama.
Saboda haka, hukumar ta bayyana cewa ya zama dole a tantance kwarewar kowane direban kwale-kwale, tare da yin rajistar duk fasinjojin da ke amfani da jiragen domin inganta tsaro a tafkunan jihar.
