Connect with us

News

Sarki Aminu Ado Bayero Ya Samu Lambar Girmamawa A Matsayin Sarki Mafi San Zaman Lafiya A Najeriya.

Published

on

IMG 20250328 WA0012 1365x2048

An karrama Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, a matsayin sarki mafi san lafiya a Najeriya. Wannan girmamawa ta fito ne daga ƙungiyar Nigerian Citizens Peace Ambassadors ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Farfesa Yahaya Imam, a wajen bikin miƙa kyautar a fadar Nassarawa Mini Palace.

Farfesa Imam ya jinjinawa Sarkin bisa jajircewarsa wajen tabbatar da zaman lafiya, musamman dakatar da gudanar da bikin Sallar Durbar don ci gaban zaman lafiya a Kano.

‘Yan Sanda Sun Cafke Mutum Biyu Da Wayoyin Sata Na Miliyan 35 A Maiduguri

“Mai Martaba Sarki yana ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan zaman lafiya. Duk da rikicin masarauta da ake fuskanta, yana ƙoƙarin tabbatar da haɗin kai da kwanciyar hankali duk da yunkurin wasu ‘yan tsiraru na haddasa rikici,” in ji shi.

Yayin miƙa kyautar, ƙungiyar Nigerian Citizens Peace Ambassadors ta bayyana cewa an yaba da irin kyawawan dabi’un da Sarkin ke nunawa, waɗanda suka ɗore tun zamanin mahaifinsa, marigayi Alhaji Ado Bayero.

A nasa bangaren, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya gode wa ƙungiyar bisa wannan karramawa, yana mai jaddada aniyarsa ta ci gaba da samar da zaman lafiya a Kano.

“Mu mutane ne masu son zaman lafiya, wannan shi ne abin da iyayenmu suka koya mana. Kano ita ce gidajenmu, kuma za mu ci gaba da bin doka da oda, muna barin komai a hannun Allah,” in ji shi.

Advertisement

Sarki ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su ci gaba da zama lafiya tare da nisantar duk wani abu da zai iya haddasa hargitsi a jihar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending